An sanar da cewa wani jirgi mai saukar ungulu ya fado a tsibirin kudancin kasar New Zeland a kusa da birnin Kaikoura lamarin da ya yi sanadiyar rayuwar mutane biyu da kuma raunanan wasu uku.
Kamar dai yadda jaridar New Zealand Herald ta rawaito jirgin mai saukar ungulu dauke da mutane biyar tare da yara ya fado ne kusa da birnin Clarence.
Mutum biyu sun raunana inda uku kuma suka ji munanan raunuka sakamakon hatsarin.
Tuni dai ma'aikatan kashe gobara, 'yan sanda, da masu bayar da agajin gaggawa a biranen Christchurch, Nelson da Wellington sun kai dauki a yankin.
A gefe guda kuma hukumar sararin samaniyyar kasar ta fara bincike akan afkuwar lamarin.