Fararen hula 3 sun rasa rayukansu, wasu 3 sun samu raunuka sakamakon hari ta sama da jiragen saman yakin Rasha suka kai a yankin Idlib da aka haramta kai rikici a cikinsa.
Ofishin Sanya Idanu na Soji 'Yan Adawa ya bayyana cewar jiragen na Rasha sun kai hari da bama-bamai sama da 20 a yankin na Idlib.
Daraktan Kungiyar Kare Hakkokin Fararen Hula Mustafa Hac Yusuf ya bayyana cewar an kashe fararen hula 2 a kauyen Movzara sannan an kashe mutum 1 a Dayr Sunbul.
Ana ci gaba da kula da lafiyar fararen hula 3 da aka kai su asibiti bayan sun samu raunua sakamakon hare-haren.
Haka zalika an bayyana ana ci gaba kokarin kubutar da mutane a yankunan.
An aiyana yankin Idlib a matsayin yankin da ba za a yi rikici a cikinsa ba a wajen taron da Turkiyya, Rasha da Iran suka gudanar a Astana Babban Birnin Kazakistan a tsakanin ranakun 4 da 5 ga Mayun 2017.
Amma duk da wannan yarjejeniya da aka cimma, Rasha da gwamnatin Asad na ci gaba da kai wa fararen hula hare-hare a yankunan.