Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar jiragen sama na soji guda 2 a jihar Helmand da ke kudancin Afganistan.
Ma'aikatar Tsaro ta bayyana cewar jiragen samfuran "Mİ-17" mallakar Rundunar Sojin Saman kasar ne kuma sun fado jim kadan bayan tashin su daga gundumar Nave da ke Helmand.
An bayyana cewar jiragen sun fado sakamakon matsala da injinansu suka samu, kuma mutane 9 da ke cikinsu sun mutu.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewar jiragen saman sun dauki sojoji da suka samu raunuka a Nave kuma sun yi karo da juna inda sama da sojoji 10 suka mutu.