Wani jirgin kasa mai gudun wuce sa'a da ya tashi daga garin Munich na Jamus ya yi karo da jirgin kasan kewaye a cikin gari a kasar Chek inda mutane 2 suka mutu, wasu sama da 40 kuma suka samu raunuka.
Mahukunta sun bayyana cewa, hatsarin ya afku a kusa da garin Domazlice da ke yammacin Chek, an dauki mutane 4 da suka samu munanan raunuka da jirgin mai saukar ungulu zuwa asibiti, wasu 7 sun samu kulawa nan take inda sauran 31 kuma suka samu 'yan raunuka kadan.
Ministan Sufuri Karel Havlicek ya bayyana cewa, duk da umarnin "Tsaya" da aka baiwa jirgin kasa tsoho samfurin "Ex 351" amma ya ci gaba da tafiya wanda hakan ya anya shi karo da jirgin mai gudu.
Kamfanin dillancin labarai na CTK ya rawaito jami'an agajin gaggawa na cewa, an aika da jiragen sama masu saukar ungulu 4 zuwa wajen.