Jimillar Falasdinawa 253 Isra'ila ta kashe a Zirin Gaza

Jimillar Falasdinawa 253 Isra'ila ta kashe a Zirin Gaza

Wasu Falasdinawa 2 da Isra'ila ta jikkata a hare-haren da ta kai Zirin Gaza sun yi Shahada a asibitin da ake kula da su.

Jami'an Kungiyar Kare Fararen Hula sun bayyana cewa, a lokacin da suke gudanar da aiyukan kwashe buraguzan gine-ginen da suka rushe a yankin Han Yunus, sun gano jikkunan mutane 4.

Rubutacciyar Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin da ke Zirin Gaza ta fitar ta bayyana cewa, tare da karin mutanen 6, jimillar mutanen da Isra'ila ta kashe a hare-haren da ta kai ya tashi zuwa mutane 253. Shahidan sun hada da yara kanana 66 da mata 39.

A ranar 10 ga watan Mayu Isra'ila ta fara kai hare-hare Zirin Gaza, kuma ta dakatar da hakan bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a ranar 21 ga Mayu.

A gefe guda, sojojin Isra'ila sun harbi wani yaro dan shekaru 16 a kusa da unguwar Talmon da Yahudawa suka mamaye da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan bisa zargin sa da jefa musu dutse.

Yaron ya ji ciwo a wuyansa, kuma an yi masa aiki inda aka sanar da yana samun sauki sosai.

A yankin Bayt Hanina da ke arewacin Kudus, 'yan sandan Isra'ila sun kama wani yaro Bafaladdine mai shekaru 10.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, 'yan sandan sun rike yaron na tsawon lokaci a motarsu, daga baya kuma suka sake shi.

Ba a bayyana me ya sa aka kama yaron Bafalasdine ba.


News Source:   ()