Takardar kuɗin ta chachos da gwamnan yankin na La Rioja mai ƙwarƙwaryar ƴanci ya ƙaddamar tuni ta fara bazuwa a tsakanin al’umma inda aka fara hada-hada da ita a wani yanayi da gwamna Ricardo Quintela na jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi ya sha alwashin bata kariya don shiga hatta kasuwar hada-hadar kuɗaɗen ketare na Argentina bayan ƙaddamar da ita a Litinin ɗin da ta gabata.
Yankin na La Rioja na sahun ƴan gaba-gaba da suke ji a jikinsu game da durkushewar tattalin arzikin ƙasar ta kudancin Amurka yayinda tsare-tsaren shugaba Javier Milei mai tsattsauran ra’ayi da ya kai ga zaftare yawan kuɗaɗen shigar da yankuna ke samu ya sake ta’azzara matsaloli masu alalaƙa da tsadar rayuwa baya ga hauhawar farashi a yankin.
Gwamna Ricardo Quintela ya ɗauki matakin sauyawa yankin kuɗinsa da nufin farfaɗo da tattalin arzkin da ya fuskanci koma baya da kuma sassauto da radadin da al’ummar yankin ke ji sakamakon hauhawar takardar kuɗin dalar Amurka kan peso na Argentina a wajen musaya.
Daga bara zuwa bana Argentina ta karya darajar Peso da fiye da kashi 60, dalilan da suka tsawwala rayuwa a ƙasar tare da haddasa hauhawar farashin kayaki musamman waɗanda ake shiga da su ƙasar.
Ƙarƙashin sabuwar dokar da gwamnan na La Rioja ya gabatar bayan kaddamar da kudin ya bayyana cewa ma’aikata za su rika karbar albashin fiye da chachos dubu 50 da ke matsayin dala 40.
Tuni dai aka fara hada-hada da sabuwar takardar kudin wadda ake sanyawa rai a nan gaba ta iya ɗara darajar takardar kuɗi ta Peso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI