Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa kasarsa za ta cigaba da kasancewa akan gaskiya zata ci gaba da kasancewa tare da Azabaijan.
Erdogan, akan zagayowar shekara ta 29 da kisan Khojaly, a shafin sada zumuntansa na twitter ya wallafa sako kamar haka,
"Muna masu addu'ar samaun rahamar Allah ga 'yan uwanmu a Khojaly a Azabaijan da aka yiwa kisan kiyashi shekaru 29 da suka gabata"
Ya kara da cewa duk da shekaru da dama sun gabata dai bamu manta da kisan kiyashin da aka yiwa 'yan uwanmu a Azabaijan ba da suka hada da yara, tsaffi da mata harsu 613. Muna masu mika sakon ta'aziyya ga kasar Azabaijan ga kuma 'yan uwan wadanda aka yi kisan gilla shekaru 29 da suka gabata. Zamu ci gaba da kasancewa kasa biyu, al'umma daya da kasar Azabaijan.