Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare -haren ta'addanci da DAESH/Khorasan suka kai a Kabul babban birnin Afghanistan kusa da filin jirgin saman birnin.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga dukkan bangarorin dake Afganistan da su mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma kare fararen hula.
Sanarwar da ta yi Allah wadai da harin, wanda da gangan aka kai hari kan fararen hula da ma’aikatan da ke taimaka wa kwashe fararen hula, majalisar ta bayyana cewa ya kamata a hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa da masu ba da kudi kan wadannan munanan hare -hare.
A yayinda aka yi kira ga dukkan bangarorin Afghanistan da su ba da damar kwashe fararen hula cikin aminci, majalisar ta jaddada cewa bai kamata yankin Afghanistan ta zama wa ta wuri da ke barazana ga kowace kasa ba ko kuma a yi amfani da ita wajen kai hari kan wata kasa ba.