Kakakin fadar gwamnatin Argentina Manuel Adorni ya rubuta a shafin sa na X cewa, an nada Gerardo Werthein tsofan jakadan kasar a Amruka amatsayin saban ministan harakokin waje jim kadan bayan amincewa da kudirin Majalisa Dinkin Duniya da Amruka ta gabatar na sake lafta takun-kumi kan kasar Cuba wanda ya samu amincewa kasashe 187 in banda kasashen Amruka Israi’la da ita kanta Arjentina.
Saban ministan harakokin wajen Gerardo Werthein ya kasance baban dan kasuwa kana ya taba zama mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar Olympics a Argentina tsakanin shekara 2009 zuwa 2021 kahin daga bisani shugaban kasar Argentina Javier Milei ya nada shi amatsayin jakadan kasar a Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI