Jaridar FOX ta sanar da Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen Amurka

Jaridar FOX ta sanar da Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen Amurka

A wasu bayanai da kawo yanzu jaridar ta FOX ce kadai ta wallafa, sun bayyana cewa Donald Trump ya doke Kamala Harris tare da zama shugaba ƙasar Amurka na 47 a zaben da al’ummar kasar suka kadawa kuri’a jiya Talata.

Wannan nasarar ta mayar da Trump shugaba na farko da ya jagoranci Amurka sau biyu amma ba a jere ba tun bayan Grover Cleveland a 1892.

Trump ya lashe zaben Amurka karon farko a shekarar 2016 inda ya doke Hillary Clinton amma kuma ya sha kaye a hannun Joe Biden yayin zaɓen ƙasar na shekarar 2020, shan kayen da ake alaƙantawa da annobar Covid-19 da ta ɓullo a wancan lokaci.

Tsawon shekaru 2 Trump ya share ya na yaƙin neman zaɓe bisa alƙawarin sake ƙarfafa Amurka.

Sai dai duk da wannan bayanai na FOX har yanzu mahukuntan Amurka basu sanar da nasarar Trump a hukumance ba, inda alƙaluma ke nuna ya na kan gaba a yawan wakilan zaɓe da ake kira Electoral Vote.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)