Jamus ta “tsaurara” dokar hana fitar da makamai zuwa Saudiyya har zuwa karshen shekarar 2021.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran Jamus (DPA) ya rawaito, gwamnatin Jamus ta bayyana cewa ba za ta bayar da izinin siyarwa kasar Saudiyya makamai ba har izuwa karshen 2021.
Bugu da kari an kuma soke izinin da aka baiwa wasu na siyarwa Saudiyya da makaman.
Kasar Jamus ta dakatar da siyarwa Saudiyya makamai ne a shekarar 2018 sakamakon yakin da take jagoranta a Yaman da kuma kashe dan jarida Jamal Kashoggi.
Gwanmatin Jamus dai ta kara wa'adin da ta diba na hana siyarwa Saudiyya ko wani irin makami.