Jami'an tsaron Pakistan sun katse hanyoyin sadarwa na internet da wayar hannu sabili da 'yan adawa

Jami'an tsaron Pakistan sun katse hanyoyin sadarwa na internet da wayar hannu sabili da 'yan adawa

An hana Khan tsayawa takara a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu,zaben da dubban yan kasar ke cewa an tafka magudi.

Jam'iyyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) ta yi fatali da matakin da aka dauka inda ta bayyana cewa za ta  ci gaba da gudanar da zanga-zanga akai-akai. Masu fafutuka na PTI sun fara tuki zuwa Islamabad a jiya Juma'a daga tashar wutar lantarki da ke arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa, amma sun hadu da shingayen yan sanda da kuma hayaki mai sa hawaye.

Wasu daga cikin magoya bayan jagoran yan adawan Pakistan Wasu daga cikin magoya bayan jagoran yan adawan Pakistan AP - W. K. Yousufzai

Ga Amnesty International, yanke hanyoyin sadarwa tamkar tauye hakkin mutane na 'yancin fadin albarkacin baki.

Jagoran yan adawa na Pakistan Imran Khan Jagoran yan adawa na Pakistan Imran Khan © AAMIR QURESHI / AFP

"Wadannan hane-hane wani bangare ne na murkushe 'yancin yin zanga-zanga a Pakistan." Fiye da shekara guda da ta gabata, Imran Khan, mai shekaru 71, ciki har da hudu a matsayin Firaminista kafin a kama shi, an tsare shi - saboda ya rasa goyon baya,na sojojin da ke da karfi a cewar masana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)