Jami’an tsaron kasar Turkiyya sun yi nasarar kame ‘yan ta’addan Daesh 14 da kuma lalata wajen horar da mambobinsu dake yankunan yammacin gundumar Adana.
Jami’an ‘yan sanda dake aiki a fannin yaki da ta’addanci sun kaddamar da farmaki akan ‘yan ta’addan ne bayan mai gabatar da kara ya bayar da umarnin daure wasu mutum 9 da aka kama da laifin aiki a kungiyar ta’addar Daesh a Siriya da Iraki.
Kanfanin dillancin labaran Ihlas ya rawaito cewa biyar daga cikinsu ‘yan kasar Siriya ne inda hudu daga cikinsu kuma ‘yan kasar Iraki ne.
Daga cikin ‘yan ta’addan daga Siriya sun hada da Ahmed Al M., 21; Muhammad Walid Al A., 24; Rabia O., 46; Ahmad Sh., 24 da dan uwansa Muhammad Sh., 29. ‘Yan kasar Iraki kuwa sun hada da Abdurrahman Raad B., 22; Sabet Tabban Mari M., 47; Abdurrahman H., 21 da dan uwansa Ali H., 37.