Matakin ya biyo bayan tutsun da shugaban ya yi tare da ƙin miƙa wuya ga jami’an tsaro da suka yi wa fadar ƙawanya.
Jami’an tsaron da suka share tsawon awanni 6 suna ƙoƙarin kamashi, sun gamu da tirjiya daga shugaba.
Yoon Suk Yeol na fuskantar binciken aikata manyan laifuka a ƙasar ta Koriya ta Kudu sakamakon dokar ta ɓaci da ya sanya wadda ta haddasa bada umarnin kamashi.
Ofishin bincike kan cin hanci ga manyan jami’a a ƙasar ya ce da alamu ba za a iya aiwatar da umarnin kama shugaban Koriya ta Kudu ba, saboda jan daga da aka yi tsakanin magoya bayansa da jami’an da suke bashi kariya da kuma ƴan sandan da suka je kamashi.
Jami’an bincike da ƴan sanda sun yi wa magoya bayan shugaban ƙasar zobe da suka yi dandazo a kusa da fadar Yoon inda suka yi iƙirarin dakatar da kama shugaban da rayuwarsu.
Jami’an dake jagorantar masu bincike sun isa fadar shugaban Koriya ta Kudu misalin ƙarfe 7 na safe agogon ƙasar da ya yi daidai da ƙarfe 10 na dare agogon GMT domin kama shugaban, to sai dai sun iske tarin jami’an tsaron fadar shugaba Yoon sama da 200 inda suka hanasu kama shi.
Bayan binciken da ake yi wa shugaba Yoon Suk Yeol yanzu haka ana ci gaba da sauraron shari’ar da aka shiga gaban kotu kan tsigeshi da aka yi daga kan mulki.
Hukuncin da kotun za ta yanke shine zai tabbatar da tsige shi ko kuma mayar da shugaban kan karaga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI