Jami’an tsaron ruwa na kasar Turkiyya sun kubutar da wasu karin masu neman mafaka 13 a cikin kwale-kwalen roba a yankin tekun dake kudu maso yammacin kasar.
Kamar yadda rundunar jami’an tsaron ruwan ta sanar masu neman mafakan sun nemi akawo musu dauki a lokacin da injimin kwale-kwalen nasu ya daina aiki a daidai lokacin da suke yankin Mugla dake kasar Turkiyya.
Bayan kubutar dasu an mikasu ga ofishin hukumar ‘yan gudun hijira domin daukar mataki na gaba.
Turkiyya dai ta kasance kasar da ‘yan gudun hijira ke yawan bi domin shiga Nahiyar Turai, musanman wadanda suka gujewa yaki da cin zarafi daga kasashensu. Kawo yanzu akwai masu neman mafaka kusan miliyan hudu da suka hada da Siriyawa miliyan 3.6 a kasar Turkiyya.