Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi tir da matakin Isra'ila na kaiwa asibitoci hari

Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi tir da matakin Isra'ila na kaiwa asibitoci hari

A cikin wata sanarwa da suka fitar, sun ce hare-haren da Isra’ila ke kai wa asibitocin da ke yankin Gasa ya saɓawa dokokin kula da lafiya na ƙasa da ƙasa, wanda kuma ke ƙara jefa rayukan mutane cikin barazana.

Isra’ila dai ta daɗe tana ƙaryata zargin da ake mata ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa wajen kai hari cibiyoyin kula da lafiya, inda ta ke kafa hujja da cewar mayaƙan Hamas na amfani da asibitocin ne a matsayin mafaka, iƙirarin da tuni dai Hamas ta ƙaryata.

A harin  baya-bayan da Isra’ila ta kai asibitin Kamal Adwan wanda shi ne kadai asibiti a yankin Arewacin Gaza ke aiki yadda ya kamata, ta ce ta kashe sama da mutane 20 daga cikin waɗanda ta ke nema, sannan kuma ta kulle sama da 240 ciki harda babban daraktan asibitin Hossam Abu Safiyeh a cikin asibitin, wanda ta bayyana a matsayin mamba a ƙungiyar Hamas, iƙirarin da tuni  Hamas ta ƙaryata.

To sai jami’an na Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi tir da matakin da Isra’ila ta ɗauka, tare da buƙatar ta gaggauta sakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)