Wata ƙungiyar Amurka da ke sanya idanu kan halin da ake ciki a Syria da ta jagoranci aikin gano makeken ƙabarin ta bayyana cewa ƙabarin guda ne cikin ƙaburbura 5 da ke ɗauke da dubunnan ɗaruruwa wanda zuwa yanzu aka gano a cikin ƙasar ta Syria.
A cewar Mouaz Moustafa, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, an gano ƙabarin na baya-bayan nan ne a yankin Qutayfah mai tazarar mil 25 daga arewacin birnin Damascus fadar gwamnati.
Dubunnan ɗaruruwan ƴan Syria ne ake zargin gwamnatin Assad ta hallakasu a sumamen da ta kai kan masu zanga-zangar 2011 da ya haddasa ɓarkewar yaƙin ƙasar sai dai a baya-bayan nan ne ƙungiyoyi ke ci gaba da gano ƙaburburan da ake zargin gwamnatin ta gina don ɓoye gawarwakin.
Nasarar gano wannan ƙaburburan na zuwa a dai dai lokacin da ƙasashe ke rige-rigen kai ɗauki ko kuma ƙulla alaƙa da sabuwar gwamnatin Syriar wadda ƴan tawaye suka kafa ƙarkashin jagorancin Abu Mohammed al-Julani da Firaministanshi Mohammed al-Bashir.
Ko a yau Talata sai da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa a ƙage ta ke kai ɗauki wannan ƙasa ta gabas ta tsakiya duk da yadda ta kaste dukkanin agajinta ga ƙasar a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI