Jami'ar Al-Azhar ta yi tir da Allah wadai ga kalaman shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron akan Islama.
Jami'ar ta Al-Azhar dake Misira ta bayyana kalaman Macron a mtsayin nuna wariyar launin fata.
Cibiyar Bincike akan Harkokin Islama ta jami'ar Al-Azhar ta bayyana cewa kalaman shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron kalami ne dake kalubalnatar Islama ba da wata jujja ko dalili ba.
Ta kara da cewa "Muna masu matukar nuna kyamar wadan nan kalaman kuma wannan kalamai ne da zasu haifar da tada zaune tsaye a cikin al'umman Musulmi"
A jawabinsa mai taken "Yaki da Ta'addancin Islma" a kasarsa Macron ya bayyana cewa a halin yanzu "Musulci ko ina a fadin duniya na cikin rikici"