Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kubutar da 'ya gudun hijira 21 daga cikin teku a yankin garin Seferihisar dake karkashin gundumar Izmir.
Jirgin ruwan roba tare da 'yan gudun hijirar da ke kokarin zuwa kasashen waje ba bisa ka'ida ba ya kusa nutsewa a yankin tekun dake kusa da Seferihisar saboda matsalar injin sa.
An nemi jami'an tsaron ruwan Turkiyya su kai dauki inda a cikin kankanen lokaci suka kai yankin inda suka kubutar da 'yan gudun hijira 21 gabanin jirgin roban ya nutse.