Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kara kubutar da wasu 'yan gudun hijirar da Girka ta kora cikin teku har su 44 a yankin Bahar Aswad.
Jami'an tsaron sun kai dauki bayan sun samu labarin cewa 'yan gudun hijiran dake cikin kwale-kwalen roba da daf ga nutsewa a yankin tsibirin Ciplak.
A yayinda 'yan gudun hijirar ke yunkurin isa tsibirin Midilli na dakarun Girka suka fasa kwale-kwalen robarsu tare da korasu cikin teku.
Jami'an tsaron Turkiyya da suka kubuatar dasu sun garzaya dasu zuwa tsibirn Junda.
An taimakawa 'yan gudun hijira a da suka hada da yara da mata da kayayyakin abinci, sutura da magani.