Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun sake kubutar da wasu 'yan gudun hijira 42 da dakarun Girka suka kora zuwa tekun yankin garin Kuşadası dake karkashin lardin Aydin.
Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kai wa 'yan gudun hijirar dauki bayan samun bayanan sirri da cewa akwai wasu baki masu neman mafaka da ke neman a kubutar dasu cikin teku.
Jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kubutar da masu neman mafakar a cikin teku su 42.
Bayan bincike, an mika masu neman mafakar ga hukumar kula da 'yan gudun hijirar kasar Turkiyya.