Jam'iyyar Democrat a Kanada ta yi kira da a daina siyarwa Isra'ila da makamai

Jam'iyyar Democrat a Kanada ta yi kira da a daina siyarwa Isra'ila da makamai

Sabuwar Jam’iyyar Democrat, wacce ita ce jam’iyya ta 4 mafi girma a Majalisar Tarayyar Kanada, ta nemi firaiminista Justin Trudeau da ya dakatar da sayar wa Isra’ila makamai har sau sun dakatar da mamayar yankunan Falasdinawa.

A cikin rubutun yakin neman sa hannu da Sabuwar Democrat Party ta gabatar a bainar jama'a kan batun ta bayyana cewa,

"'Yan kasar Kanada sun damu matuka da yadda' yan sandan Isra'ila suka mamaye Masallacin Al-Aqsa da kuma karuwar tashin hankali a Sheikh Jarrah, bayan makonni na tashin hankali a Gaza tare da mamaye Gabashin Kudus don tilastawa Falasdinawa ficewa daga yankin"

A cikin sanarwar, wacce ta nuna cewa ya kamata a kare rayukan fararen hula, an lura da cewa ya kamata a yi Allah wadai da kowane irin rikici, da hargitsi da tashin hankali.

Haka kuma sanarwar da Jam'iyyar ta New Democrat ta fitar ta kara da cewa,

"A duk lokacin da aka yi hargitsi irin wannan farar hula ne suka fi shan wahala da kasancewa cikin halin ha'u'la'i. Ana bukatar a rage tashin hankali cikin gaggawa don hana ci gaba da rasa rayukan. Dukkanin Falasdinawa da Isra'ilawa na da 'yancin rayuwa cikin aminci da tsaro. Har ila yau don rage tashin hankali da kuma neman mafita cikin adalci da lumana. "Dole ne Kanada ta taka rawa mai karfi," yanzu lokaci ya yi da za a daina sayar wa Isra'ila makamai har sai ta daina mallakar kasa a  haramtacciyar hanya."


News Source:   ()