Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Ahmed al-Sharaa, ta naɗa Murhaf Abu Qasra jigo a ƙungiyar HTS, da ta jagoranci rikicin da ya kifar da gwamnatin Bashar al-Assad, a matsayin ministan tsaro.

Ba za mu barar makamai a hannun jama'a ba, ko daga ɓangaren ƴan tawaye ko kuma a ɓangaren mayaƙan Kurdawa na SDF.

Fira ministan Syria Mohammed al-Bashir ya ce a wannan makon ne za a sake fasalin ma'aikatar tsaron ƙasar, ta hanyar shigar da ƙungiyoyin ƴan tawayen da suka kifar da Assad da tsofaffin jami'an sojin gwamnatinsa cikin rundunar sojojin ƙasar.

Haka nan a ranar Asabar data gabata, gwamnatin Syria ta naɗa Asaad Hassan al-Shibani a matsayin ministan harkokin wajen ƙasar, a wani mataki da sabuwar gwamnati ta Syria ke ɗauka don kulla hulɗar alaka da ƙasashe.

Sakamakon irin makatan da gwamnatin ke ɗauka dai ya sanya mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka Barbara Leaf, ta sanyan da matakin Amurka na janye batun bada tukuicin dala miliyan 10 da a baya ta sanar ga duk wanda ya taimaka da bayanan da suka kai ga kama Ahmed al-Sharaa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)