An bayyana cewa birnin Istanbul ce ta fi yawan al'umma daga cikin biranen Nahiyar Turai a shekarar 2021 inda birnin Moscow ke bin ta baya.
Dangane da bayanan da kamfanin dillancin labaran Ajans Press ya samo daga bayanan Statista, an bayyana biranen da suka fi yawan jama'a a Turai a 2021.
Don haka, an bayyana cewa Istanbul ya dauki wuri na farko tare da yawan jama'arta da ke kusan miliyan 16. Moscow, babban birnin Rasha, ita ce ta biyu a jerin, sai Paris daga Faransa a matsayi na uku, London (babban birnin Ingila) a matsayi na hudu sai Madrid (babban birnin Spain) a matsayi na biyar.
Idan aka duba birane 20 mafi yawan al'umma kasar Birtaniya ce aka fi samun yawan biranen dake da yawan jama'a akan haka an lura da cewa Manchester ta dauki matsayi na 14, Birmingham na 15 da Leeds zuwa na 20.