Wannan na zuwa ne, daidai lokacin da wani harin saman Isra’ilan ya kashe Falasdinawa 10 a garin ammun da ke Gabar Yammacin Kogin Jodan, yayin da dakarun gwamnatin Yahudun ke ci gaba da kai farmaki yankunan da aka mamaye.
Sama da Falasdinawa 500,000 ne suka koma arewacin Gaza tun daga lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kama aiki, inda suke jiran agajin jin kai daga hukumomin kasa da kasa.
A yau ne haramcin da Isra'ila ta yi wa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA a yankin Gabashin Kudus da Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye zai fara aiki a hukumance.
Tun daga lokacin da Isra’ila ta fara yaki a Gaza, ranar 7 ga Oktoba, 2023, akalla Falasdinawa 47,417 ne suka mutu, inda 111,571 suka jikkata, yayin da aka kashe mutane 1,139 a Isra'ila bayan hare-haren da Hamas ta jagoranta a wannan rana inda ta yi garkuwa da sama da mutum 200.
A halin yanzu motocin kungiyar agaji ta Red Cross sun isa Khan Younis domin mika Yahudawwa biyu da ke tsare a hannun Hamas.
Falasɗinawa 90 ne suka isa gida bayan da mahukuntan Isra’ila suka sake su ƙarƙashin yarjejeniyar da Hamas ta saki Yahudawa 3 tun a ranar 19 ga watan Janairun 2025.
Haka zalika, a ranar 25 ga Janairu kuma, Falasdinawa 200 suka shaki iskar ‘yanci daga gidajen yarin Isra’ila, bayan sakin wasu sojoji hudu da Hamas ta yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI