Isra'ila ta yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi - Amnesty

Isra'ila ta yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi - Amnesty

Ƙungiyar ta Amnesty International mai cibiya a birnin London ta ce, ta gudanar da bincike ne ta hanyar amfani da hotunan da aka ɗauka da tauraron ɗan Adam da kuma baza jami’anta a yankin da suka tattaro rahotanni daga mutanen Gaza. Kazalika ta kafa hujja da  abin da ta kira miyagun kalaman da ke fitowa daga bakin gwamnatin Isra’ila da sojojinta.

Sai dai tuni Isra’ila cikin fushi ta yi watsi da wannan rahoton da ta bayyana a matsayin ƙaryar da aka ƙirkira.

Shugabar Amnesty, Agnes Callamard ta zargi Isra’ila musguna wa Falasɗinawa tamkar ba ƴan adam ba waɗanɗa ko kaɗan ba su da gatar kare hakkokinsu da mutuninsu.

Callamard ta ce, dole ne sakamakon binciken nasu ya zama tamkar gagarumin kira ga ƙasashen duniya kan cewa, abin da ke faruwa a Gaza, kisan ƙare dangi ne wanda kuma ya zama tilas a kawo ƙarshensa.

Kimanin mutane dubu 44 da 580 ne suka rasa rayukansu a Gaza akasarinsu fararen hula tun bayan barƙewar yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoban bara, bayan Hamas ta yi luguden wuta kan Isra’ila da ya yi sanadiyar mutuwar dimbin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)