Tun farko Isra’ila ta yi zargin cewa mayaƙan Hamas na amfani da gidajen jama’a da ke yankin na kudanci da tsakiyar Gaza don zame musu mafaka da suke amfani da su wajen kai hare-hare ga Sojin na Tel Aviv.
Mazauna yankunan sun ce sun samu saƙonnin kar ta kwana baya da takardun umarnin ficewa da jiragen yaƙin Isra’ilan ke zubo musu ta sama da ke neman lallai su gaggauta ficewa daga muhallansu, wanda ke nuna ilahirin al’ummomin yankunan kudancin birnin Khan Younis da gabashin Deir Al-Balah za ssu fice daga matsugunansu ciki har da dubbai da ke samun mafaka bayan da Isra’ilan ta korosu daga yankunansu.
A cewar Isra’ilan a baya-bayan nan ta na yawan samun hare-haren daga yankunan wanda ke nuna tabbas akwai mayakan Hamas a cikin gidajen jama’a.
Ko a jiya Alhamis sai da jiragen yaƙin Isra’ilan suka yi luguden wuta kan al’ummar yankin Kissufim a Khan Younis bayan zargin cewa an harbo mata roket ta yankin.
Umarnin sake kwashe Falasɗinawan na zuwa ne a dai dai lokacin tattaunawa ke gudana a Qatar wadda ake da fatan iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ko kuma kawo ƙarshen yaƙin na fiye da watanni 10 wanda ya raba kusan ilahirin al’ummar Gaza miliyan 2.3 da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI