Alkaluma sun bayyana cewar daga ranar 7 g awatan Oktobar da mayakan Hamas suka kai hari a kan Yahudawa, Israilar ta kaddamar da yakin daukar fansar da ya hallaka mutane dubu 46 da 913, yayin da wasu sama da dubu 100 da 750 suka jikkata, kamar yadda alkaluman hukumar Falasdinu suka bayyana.
Cikin shugabannin Falasdinawan da Isra'ila ta hallaka sun hada da Yahya Sinwar da Ismail Haniyeh da Mohammed Deif ko kuka Ibrahim Al Masri, tare da Marwan Issa da kuma Saleh Al Arouri.
Ismaïl Haniyeh AFP - FADEL SENNAWadannan na daga cikin fitattun kwamandodin Falasdinwa dake da karfin fada a ji wajen fafutukar 'yantar da yankin Falasdinu.
Baya ga rasa dimbin rayukan da aka samu a yakin, Isra'ila ta yi nasarar ragargaza akalla kashi 70 na yankin Gaza, matakin da ya sanya dubban Falasdinawa rasa muhallin su da kuma tilasta musu barin yankin.
Rahotanni sun ce har yanzu akwai gawarwakin Falasdinawa da dama kwance a karkahsin burabuzan gidajen da suka rushe amma ba a iya kaiwa gare su domin zakulo su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI