Isra'ila ta tagayyara ƙananan yara fiye da dubu 400 a Lebanon- UNICEF

Isra'ila ta tagayyara ƙananan yara fiye da dubu 400 a Lebanon- UNICEF

Dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da faɗaɗa hare-harenta a Lebanon da sunan yaƙar dakarun ƙungiyar Hezbollah, UNICEF ta ce rayuwar dubban ƙananan yara na ci gaba da faɗawa a haɗari sakamakon tagayyarar da suke yi bayan da hare-haren Isra’ilar ya tilasta musu barin matsugunansu.

Mataimakin babban daraktan UNICEF a ɓangaren ayyukan jinƙai Ted Chaiban, ya yi gargaɗin cewa wannan yaƙi da Isra’ila ta faro a Lebanon kai tsaye ya tagayyara tsarin ilimin ƙasar bayan da ya tilastawa yara aƙalla miliyan 1 da dubu 200 barin makarantu.

A cewar jami’in galibin makarantun da ke wannan yanki sun fuskanci hare-hare daga Isra’ila wanda ko dai ya lalata su ta yadda ba za a iya karatu ba ko kuma ya firgita yaran da ke yankin ta yadda suka gudu zuwa wasu yankuna don tsira da rayukansu.

UNICEF akwai aƙalla asibitoci 12 da hare-haren Isra’ilar ya shafa a yankin na kudancin Lebanon mai iyaka da Isra’ila wanda ya jefa rayuwar tarin ƙananan yara a haɗari.

Kawo yanzu dai fiye da mutane dubu 2 da 300 Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta ke kaiwa Lebanon da kaso mai yawa na mata da ƙananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)