Isra'ila ta tabbatar da kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar

Isra'ila ta tabbatar da kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar

Tun da farko Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike domin tantance kwayoyin halittan shugaban na Hamas kafin tabbatar da mutuwarsa.

Sai dai sakamakon farko-farko na gwajin kwayoyin halittar ya nuna cewa, Sinwar ɗin ne Isra'ila ta kashe kamar yadda ta tabbatar wa Amurka.

Isra'ila ta ɗauki gawar Sinwar zuwa Birnin Kudus domin gudanar da bincike a kanta bayan harin da ta kai cikin wani gida da shugaban na Hamas da muƙarrabansa ke ciki.

Kazalika rundunar sojin Isra'ilar ta ce, babu wata alamar cewa, akwai Yahudawa da ake garkuwa da su a ginin da ta ƙaddamar da farmakin na yau Alhamis.

Kodayake har ya zuwa wallafa wannan rahoton, ƙungiyar Hamas ba ta fitar da wata sanarwa ba da ke tabbatar da mutuwar Sinwar ko kuma akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)