
Daga cikin tsoffin fursunonin har da ɗaruruwan da aka kama a yankin bisa zarginsu da kai harin 7 ga watan Oktoban 2023 a kudancin Isra'ila, inda aka ci gaba da tsare har tsawon watanni ba tare da tuhuma ba.
Daga cikin waɗanda suka shaƙi iskar ‘yancin, akwai maza 445, matasa 21, da mace guda, bisa ga alƙaluma da kuma jerin sunayen da jami’an Falasdinawan suka fitar, amma ba a bayyana shekarunsu ba.
A wannan karon, Falasɗinawa 50 aka sako a yankin yammacin gaɓar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Ƙudus da ke fuskantar mamaya daga dakarun Isra’ila.
Sakin nasu ya zo ne bayan da Hamas ta mika gawarwakin wasu Yahudawa hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross.
Isra'ila ta jinkirta mika fursunoni sama da 600 tun ranar Asabar domin nuna adawa da abin da ta bayyana cin zarafin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Hamas dai ta kira jinkirin da aka samu a karshen mako a matsayin rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ta yi fatali da shirin sake zaman tattaunawa, bisa sharaɗin sai an sako fursunonin.
Har yanzu dai ba a san makomar tattaunawar da za a sake yi ba, wadda ake fatan za ta kai ga kawo ƙarshen wannan yaƙin da ya yi ajalin dubub dubatar Falasdinawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI