Isra'ila ta kashe sama da mutane 270 a Lebanon

Isra'ila ta kashe sama da mutane 270 a Lebanon

Rundunar Sojin Isra'ila ta ce ta kai sama da hare-hare 300 a kan Hezbollah, yayin da ta yi kira ga mazauna kudancin Lebanon ɗin da su fice daga yankin saboda tana shirin ƙaddamar da wasu hare-haren kan mayakan Hezbollah.

Kazalika hare-haren na Isra'ila sun jikkata sama da mutane 400 kamar yadda Ma'aikatar Kiwon Lafiyar Lebanon ta sanar.

Sai dai ita ma ƙungiyar Hezbollah ta ce, ta kai hari kan wasu wurare uku a yankin arewacin Isra'ila.

Adadin mamata fiye da 180, shi ne mafi yawa da aka samu a wani hari da aka kai daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Yakin ya ɓarke ne bayan ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta kai hari mafi muni a kan Isra'ila, yayin da wannan yaƙin ya shafi Hezbollah da sauran ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tuni Iran ta gargaɗi Isra'ila game da abin da ka iya faruwa nan gaba bayan ƙazamin faarmakin da ta kai wa Hezbollah a babban sansaninta da ke Lebanon.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana harin na Isra'ila a matsayin 'rashin hankali'.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)