Isra'ila ta kashe mutane 1,974 a Lebanon

Isra'ila ta kashe mutane 1,974 a Lebanon

Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki a tsakiyar birnin Beirut a sanyin safiyar yau, inda ta kashe mutane 9 a wani asibiti mallakin mayaƙan Hezbollah.

Tuni sojojin na Isra'ila suka bada sabuwar sanarwa da ke ɓukatar fararen hula da su fice daga yankunan da ke kudancin Beirut gabanin ta yi luguden wuta kan wuraren da Hezbollah ke da iko da su.

Hezbollah wadda ke samun goyon bayan Iran ta ce ta fatattaki sojojin Isra'ila da suka yi yunƙurin kutsowa ta Kofar Fatima, wato tsohuwar kan iyaƙar da ke kudancin Lebanon.

A bangare guda, Ma'aikatar Kiwon Lafiyar Lebanon ta ce, harin Isra'ila ya kashe masu aikin bada agaji 40 da suka haɗa da jami'an kashe gobara a cikin kwanaki uku, amma a jumulce, masu aikin agaji 97 ne Isra'ila ta kashe a Lebanon tun bayan ɓarkewar rikicin a watan Oktoban bara.

Kodayake Isra'ila ta nanata cewa, tana ƙaddamar da hare-hare ne kan cibiyoyin bayanan sirrin mayakan Hezbollah da ke Beirut, amma ba kan fararen hula ba.

Sojojin Lebanon sun dakile harin Isra'ila

A karon farko cikin shekara guda, rundunar sojin Lebanon ta ce ta mayar da wani harin da Isra'ila ta harbo a yau Alhamis bayan wani jami'inta ya sake rasa ransa a sanadiyar hare-haren Isra'ilar.

Wani soja ya rasa ransa bayan Isra'ila ta kai hari kan rumfar sojoji da ke Bint Jbel a kudanci, abin da ya sa dakarunmu da ke bakin aiki suka mayar da martani. Inji rundunar sojin Lebanon.

Wannan ne karon farko da sojojin gwamnatin Lebanon suka mayar da martanin tun bayan ɓarkewar rikicin tsakanin Hezbollah da Isra'ila a watan Oktoban bara kamar yadda wani jami'in sojin ƙasar da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)