Isra’ila ta kashe kusan kashi 2 cikin 100 na yawan al’ummar Gaza

Isra’ila ta kashe kusan kashi 2 cikin 100 na yawan al’ummar Gaza

A cewar alƙaluman wanda kafofin yaɗa labarai da dama suka tattara ciki har da Al Jazeera, kashi 75 na yawan mutanen da Isra’ilan ta kashe yara ne da matasa ƴan ƙasa da shekaru 30.

A jumulla Sojojin Isra’ilan sun kashe Falasɗinawa dubu 39 da 790 yayinda kuma suka jikkata wasu dubu 92 da guda biyu, alƙaluman da bai ƙunshi yawan mutanen da suka ɓace waɗanda galibinsu ko dai suna tsare a hannun gwamnatin Isra’ila ko kuma sun mutu ba tare da anga gawarwakinsu ba.

Wasu Falasɗinawa lokacin da suke gudun hijira daga Khan Younis. Wasu Falasɗinawa lokacin da suke gudun hijira daga Khan Younis. REUTERS - Hatem Khaled

Kawo yanzu fiye da mutum dubu 10 ne ba a iya gano inda suke ba a sassan Gaza daga faro yaƙin na ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu.

Alƙaluman hukumar ƙididdigar sun ce fiye da kashi 70 na majinyatan da ke Gaza mata ne da ƙananan yara waɗanda hare-haren Isra’ila ke rutsawa da su.

Kusan mutum miliyan 2 ne yanzu hake ke gudun hijira bayan da Isra’ilan ta rushe gine-ginen, adadin da bai kunshi al’ummar Khan Younis da a baya-bayan aka umarci su gaggauta ficewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)