Isra'ila ta karya ƙa'idojin yarjejeniya bayan ƙin sakin Falasɗinawa 620

Isra'ila ta karya ƙa'idojin yarjejeniya bayan ƙin sakin Falasɗinawa 620

Wannan kalamai na Mardawi na zuwa a dai dai lokacin da tankokin yaƙin Isra’ila ke cigaba da kurɗawa cikin yankunan gaɓar kogin Jordan karon farko da ake ganin irin hakan cikin fiye da shekaru 20.

Tun farko dama hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ya raba mutane dubu 40 da muhallansu a yankin arewacin gaɓar ta kogin Jordan galibinsu waɗanda ke rayuwa a sansanonin ƴan gudun hijira.

Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres ya shaidawa zaman taron hukumar kare haƙƙin ɗan adan a birnin Geneva cewa wajibi ne ayi dukkanin mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen ɓarkewar yaƙi a dukkanin sassan Falasɗinu.

Sai dai ƙungiyar Islamic Jihad ta bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin dakarunta da Sojin Isra’ila a Silat al-Harithiya.

Wasu bayanai da kafar alJazeera ta fitar a safiyar yau, ta ce manyan motocin Isra’ila na ci gaba da aikin ɓarje tituna da gidaje baya ga kayakin more rayuwa a Burqin ƙari kan dokar hana zirga-zirga da ta sanya a Qabatiya da ke kudanci.

Kafofin yaɗa labarai irin CNN sun ruwaito Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na cewa a shirye ƙasar ta ke ta cigaba da kai hare-hare Gaza da sauran sassan Falasɗinawa.

A gefe guda Isra'ila ta sanar da shirin girke dakaru na tsawon shekaru a yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)