Haramcin na ƙunshe ne a cikin wata sanar da Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz ya fitar a wannan Larabar.
Duk wanda ya gaza caccakar hare-haren da Iran ta kai wa Isra'ila, to bai cancanci sanya ƙafarsa cikin Isra'ila ba- Inji Ministan Harkokin Wajen.
Ministan ya bayyana Guterres a matsayin wanda ke nuna goyon baya ga ƴan ta'adda, masu aikata fyaɗe da kashe-kashe.
Katz ya ƙara da cewa, tarihi zai tuna Guterres a matsayin dauɗa ga Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai bayyana shi da mai goyon bayan mayaƙan Hamas da Hezbollah da Huthi da kuma Iran.
Jim kaɗan da harin da Iran ta kai wa Isra'ila a yammacin jiya Talata, Guterres ya yi tur da faɗaɗar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya jaddada buƙatar tsagaita musayar wuta.
Isra'ila ta jima tana caccakar Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da alaka tsakanin ɓangarorin biyu ta yi tsami musamman bayan farmakin da Hamas ta kaddamar kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Guterres ya sha nanata buƙatar tsagaita musayar wuta a rikicin da ake fama da shi a Gaza da Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI