Jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya Danny Danon ya ce idan mayaƙan Houthi suka ci gaba da kai musu hari to za su iya fuskantar abin da ya faru da Hamas da Hizbullah da kuma Bashar Al-Assad na Syria.
Ambasada Danny Danon ya kuma gargadi Iran da cewa Isra'ila na da ikon kai hari ko ina a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da cikin Iran. domin a cewarsa ba za su lamunci hare-haren da wasu da ke samun goyon bayanta ke kai musu ba.
To sai dai bayan sa'o'i da gabatar da gargadin, sojojin Isra'ila sun ce sun samu nasarar kame wani makami mai linzami da aka harbo mata daga ƙasar Yemen.
Bayan sanar da kamen makamin da Isra’ila ta yi, shugaban majalisar ƙoli ta mayaƙan Houthi Mohamed Ali Al-Houthi, ya ce ba za su daina kai hare-haren cikin Isra'ila ba.
Kakakin mayaƙan Houthi Yahya Saree ya ce sun kai hari a filin jirgin sama na Ben Gurion da ke kusa da birnin Tel Aviv da kuma tashar wutar lantarki da ke kudancin birnin Kudus, ta hanyar amfani da makami mai linzami na Zulfiqar.
Mayaƙan Houthi dai na kai hare-hare cikin Isra’ila, a wani al’amari da suka bayyana a matsayin nuna goyon baya ga Falasɗinawan da Isra’ila ke kashewa a Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI