Isra’ila ta dakatar da kai kayayyakin agajin jin kai zuwa zirin Gaza

Isra’ila ta dakatar da kai kayayyakin agajin jin kai zuwa zirin Gaza

Wannan na zuwa ne, bayan da gwamnatin Netanyahu, ta yanke shawarar hana shigar da kayayyakin agajin jin ƙai zuwa zirin Gaza, bayan ƙarewar wa’adin farko na yarjejeniyar, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Isra’ila suka tabbatar.

Har dai yanzu Hamas ba ta ce uffan ba game da shawarar da ta bukaci a sako rabin mutanen da ake tsare da su a Gaza, ciki kuwa har da waɗanda suka mutu, amma gawarwakinsu na tsare.

Falasɗinawa a Gaza sun ce suna fargabar komawar yakin, yayin da suka fara azumin watan Ramadan mai alfarma, a cikin baraguzan gine-ginen da barnar Isra’ila ta haddasa.

Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da wani hari da jirage sama marasa matuka a birnin Beit Hanoon da ke arewacin Gaza, inda suka kashe aƙalla mutum guda tare da raunata wani.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sabunta adadin waɗanda suka mutu zuwa  61,709, yana mai cewa dubban Falasɗinawa da suka bace ana kyautata zaton sun mutu ne a karkashin baraguzan gine-gine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)