Dakarun na Isra’ila sun ci gaba da kutsawa kan iyakar ƙasar da Syria ta gefunan yankin tsaunin Hermon tazara mai nisa daga yankunan da tun farko Netanyahu ya bayyana cewa ƙasar ta ƙwace daga Damascus jim kaɗan bayan faɗuwar gwamnatin Bashar al-Assad, dukkaninsu a zagayen tuddan Golan, yankunan da kafin yanzu Isra’ilar ke riƙe da su a matsayin mallakar wucin gadi.
An ci gaba da ganin tururuwar Sojin na Isra’ila a yankin tsaunin na Hermon a wani yanayi da ƙasar ta Yahudu ke ci gaba da kai hare-hare sassan Syriar, ko da ya ke sabon jagoran ƙasar kuma tsohon ɗan tawaye Mohammed Abu Jolani da ya fito daga wannan yanki ya ce ba rikici ke gaban ƙasar a yanzu ba face yunƙurin sake ginata.
Wannan hali da ake ciki a Syria na zuwa a dai dai lokacin da ake sa ran cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza da Isra’ila a wata tattaunawa da yanzu haka ke gudana a birnin Alƙahira, ko da ya ke Isra’ilan na ci gaba da kai hare-hare sassan Gaza da ko a safiyar yau ya hallaka tarin fararen hula.
A gefe guda, tuni wasu iyalan Falasɗinawa mazauna Amurka suka maka gwamnatin ƙasar gaban kotu game da yadda ta ke ci gaba da baiwa Isra’ila makaman da ta ke amfani da su wajen aikata kisan kiyashi a Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI