Isra'ila ta ce akwai yiwuwar ta kashe shugaban Hamas

Isra'ila ta ce akwai yiwuwar ta kashe shugaban Hamas

Wannan ya biyo wani hari ne da rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar a wannan Alhamis wanda ya yi sanadiyar mutuwar Sinwar kamar yadda ake zato. Kazalika harin ya rutsa da wasu muƙarrabansa.

Wata sanarwa da Rundunar Sojin Isra'ila ta fitar ta ce,

Kawo yanzu, ba a tantance ainihin waɗannan ƴan ta'addar ba.

Kazalika rundunar sojin ta ce, babu wata alamar cewa, akwai yahudawa da ake garkuwa da su a ginin da ta ƙaddamar da farmakin na yau Alhamis.

Kodayake har ya zuwa wallafa wannan rahoton, ƙungiyar Hamas ba ta fitar da wata sanarwa ba da ke tabbatar da mutuwar Sinwar ko kuma akasin haka.

Muddin dai aka tabbatar da mutuwarsa, hakan zai kasance gagarumar nasara ga sojojin Isra'ila da kuma firaminista Benjamin Netanyahu.

A ɓangare guda, hukumomin Falasɗinu sun ce, akalla mutane 15 sun rasa rayukansu da suka haɗa da ƙananan yara biyar a farmakin da sojojin Isra'ila suka kai kan wata makaranta da jama'a ke fakewa a cikinta a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)