Netanyahu ya bayyana haka ne bayan da ya jagoranci taron majalisar ƙolin Isra’ila ta tsaro akan tayin yarjejeniyar tagaita wutar a Lebanon da masu shiga tsakanin a ƙarƙashin jagorancin Amurka suka gabatar masa.
Firaministan ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da aka daɗe ana dakon ganin an ƙulla ba za ta fara aiki ba, har sai majalisar ministocinsa ta amince da ita.
Sai dai wani abu da ya ja hankali, wanda kuma za a iya cewar ya haifar da fargaba akan makomar yarjejeniyar da tsagaita wutar shi ne gargaɗin da Netanyahu yayi kan cewa Isra’ila na da damar janyewa daga yarjejeniyar idan buƙatar hakan ta taso domin kare kanta daga duk wani lamari da ka iya kasancewa babbar barazana gareta.
Wannan ci gaba da aka samu na zuwa a yayin da Isra’ilar ke ci gaba da ɓarin wuta a sassan Lebanon da zummar neman murƙushe mayakan Hezbollah, lamarin da ya sanya ƙaruwar adadin mamata da kuma waɗanda suka jikkata a ƙasar.
Ma’aikatar lafiyar Lebanon ta ce ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, mutane fiye da dubu 3 da 750 Isra’ila ta kashe, baya ga jikkata wasu kimanin dubu 15,630 akasarinsu mata da yara, a hare-haren da take ci gaba da kai wa da sunan murƙushe ƙungiyar Hezbollah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI