
Haka zalika, Isra’ilan ta aike da tankokin yaƙi zuwa Yammacin Kogin Jordan, karon farko kenan tun bayan shekaru 23 da suka gabata.
Ofishin Firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu, ya fitar da sanarwar cewa, shirin sakin Falasɗinawa da aka shirya yi a ranar 22 ga Fabrariru, ya gamu da tsaiko, har sai Hamas ta tabbatar da cewa za ta sako Yahudawan da ke hannunta ba tare da karya yarjejeniyar da aka cimma ba.
A baya-bayan nan ne Hamas ta ce tsaikon da Isra’ila ta yi wajen sakin Falasɗinawan da ke tsare a hannunta, a karo na bakwai da aka yi musayar fursunoni tsakaninsu, ya karya yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita wuta, bayan da ta mika wa gwamnatin ta Yahudu mutane shida da ke tsare a hannunta.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da sanarwar cewa, Falasɗinawa 48,319 ne suka mutu sakamakon munanan hare-haren Isra’ila, inda sama da dubu 111 suka samu munanan raunuka.
Sanarwar gwamnatin Falasɗinu ta ce daga lokacin da aka fara wannan yaƙi kawo yanzu, aƙalla mutum 61,709 ne suka mutu, inda ake ci gaba da laluben dubun dubatar Falasdinawan da ake zargin sun mutu a karkashin baraguzan gine-gine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI