Isra'ila ta aika tawaga Masar duk karya ƙa'idojin yarjejeniyarta da Hamas

Isra'ila ta aika tawaga Masar duk karya ƙa'idojin yarjejeniyarta da Hamas

Zaman ci gaba da tattaunawa kan wannan yarjejeniya da ya rage ƙasa da makwanni 2 wa’adinta ya kawo ƙarshe gabanin shiga rukuni na 3 wanda shi ne zai bayar da damar samar da yarjejeniyar dindindin, na zuwa a dai dai lokacin da zarge-zarge ke yawaita kan Isra’ila game da yadda ta ke cigaba da karya ƙa’idodjin da ke ƙunshe a wannan yarjejeniya ciki har da hana shigar da adadin abinci da sauran kayakin agaji da aka tsara za a shigar a wannan ɗan tsakani.

Bugu da ƙari akwai gidajen wucin gadi, waɗanda ƙarƙashin yarjejeniyar ta rukuni na 2 aka tsara za a shigar da dubu 60 amma har zuwa yanzu babu ko guda da Isra’ilan ta amince aka shiga da su yankin, duk yanayi mai tsanani da ake gani a sassan Gaza.

Ci gaba da tattaunawar a birnin Alƙahira na zuwa a dai dai lokacin da Amurka ta aike da tarin makamai da manya bama-bamai ga Isra’ilan, bama-baman da tun farko gwamnatin Joe Biden ta hana shigar miƙasu ga ƙasar ta Yahudu saboda fargabar ta yi amfani da su kan Falasɗinawa amma kuma Trump ya bayar da damar bayar da su a yanzu.

A gefe guda, cikin wani jawabi da Netanyahu ya gabatar yayin ganawarsa da Marco Rubio ya ce manufar Amurka da Isra’ila shi ne wargaza shirin Iran da kuma kassara tasirinta a gabas ta tsakiya, kalaman da tuni Tehran ta bayyana su da karya dokokin ƙasa da ƙasa ƙarƙashin tanadin Majalisar ɗinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)