Isra’ila na fargaban cewa Iran ka iya kaiwa ma’aikatunta dake kasashen waje hari kasancewar yadda Iran ke tayin kalaman barazana bayan kashe masanin nukiliyarta.
Sanarwar ta bayyana cewa Iran ka iya kaiwa ma’aikatun Isra’ila hari dake kasashen dake kusa da ita da suka hada da Georgia, Azabaijan, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.
Kamar yadda ma’aikatar yaki da ta’addanci ta kasar ta sanar “Kasancewar irin barazanar da Iran ke bayyanarwa da kuma yadda ta kasance wacce ta cundanya da ayyukan ta’addanci a baya zata iya kai ire-iren wadannan harin akan ma’aikatun Israila”
Shugaban addinin kasar Iran da kuma jagoran sojojin kasar sun zargi Isra’ila da kashe masanin kimiyyarta a makon jiya. Daya daga cikin masu baiwa shugaban addinin Iran shawara ya bayyana cewa Iran zata mayar da martani akan kisan.