Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Kafafen yaɗa labarai kamar sashin Larabci na Aljazeera da Sky News sun rawaito cewa jagoran wakilan Hamas Khhalil al-Hayya ya miƙa saƙon amincewa da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar.

Kowanne lokaci daga yanzu kuma ana sa ran Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman al-Thani zai yi jawabi a wani taron manema labarai, yayin da aka samu rahotannin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a yaƙin Gaza.

Bayanan da suka fara fita kan yarjejeniyar

Tun a yammacin jiya talata kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun rawaito cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da za a cimma ta bayyana cewar Isra'ilar zata saki Falasɗinawa 50 a kan kowanne Bayahude guda da Hamas ta yi garkuwa da shi.  

Yarjejeniyar ta amince cikin kwanaki 42 na farko bayan amincewa da ita, sojojin Isra'ila za su janye daga unguwannin jama'a, yayin da za'a bai wa Falasdinawa damar komawa gidajensu a arewacin Gaza tare da kai musu kayan agaji wanda zai kunshi motoci 600 kowacce rana.

A ƙarƙashin yarjejeniyar ta farko, Isra'ila za ta ci gaba da kula da mashigin Philadelphia wanda ke iyakar Gaza da Masar duk da buƙatar kungiyar Hamas na janye dakarunta a wurin, yayin da ta amince ta janye sojojin ta da ke mashigin Netzarim.

Yarjejeniyar ta 2 za ta kunshi buƙatar Hamas ta sakin ɗaukacin sojojin Isra'ilar da take garkuwa da su domin ganin an saki wasu ƙarin Falasdinawan da ake tsare da su.

Rahotanni sun ce yarjejeniya ta 3 zata mayar da hankali a kan musayar gawarwakin sauran mutanen da aka yi garkuwa da su domin bada damar sake aikin gina Gaza na shekaru 3 zuwa 5 a karkashin jagorancin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)