Isra'ila da Hamas na shirin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zagaye na 2

Isra'ila da Hamas na shirin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zagaye na 2

Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani a Misra cewar, ta shirya domin fara tattaunawa zagaye na biyu tare da kafa sharaɗin gudanar da shi cikin sirri domin kare lafiyar wakilansu daga duk wani haɗari.

Wani daga cikin wakilan na Hamas, ya ce yanzu suna jiran masu shiga tsakani daga bangaren Isra’ila domin kawo ƙudurin tattaunawar da ake bukatar yi domin ɗorawa daga shirin tsagaita wutar na farko da aka aiwatar.

Daga cikin yarjejeniyar tsagaita wutar ta farko tsakanin Hamas da Israila akwai sakin fursunoni guda 33 na Isra’ila da kuma sako Falasɗinawa 1,900 waɗanda aka Israila ke tsare dasu.

Ana sa ran tsagaita wutar a zagaye na biyu zai mayar da hankali kan batun sakin ragowar fursunoni daga bangarorin biyu, da kuma kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya.

Ofishin Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce za a cigaba da sulhun a zagaye na biyu tare da wakilin shugaban Amurka Donald Trump a yankin gabas ta tsakiya, Steve Witkoff.

Yanzu haka dai, Netanyahu na birnin Washington DC inda ya gana da Trump, a wani yanayi da ake sa ran tattaunawarsu za ta kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Hamas wanda ya yi sanadin rayukan dubun dubatar mutane da jikkata wasu, baya ga wasu ɗaruruwa da suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)