
Blinken wanda ke shirin aje mukaminsa domin bai wa sabuwar gwamnatin Trump nada wanda zai gaje shi, ya shiadawa wasu fitattun mutane a Washington cewar rashin samun tsari mai kyau da zai maye gurbin yanayin da ake ciki bayan yakin dake gudana, tare da samarwa Falasdinawa ko kuma kungiyar hamas tsarin siyasa mai kyau, ana iya samun bullar wata kungiya mafi hadari da ka iya tasowa a yankin.
Sakataren ya bukaci sanya ikon yankin Gaza a karkashin shugabancin hukumar Falasdinawa wadda yanzu haka ke da rauni wajen ikon da take da shi wajen jagorancin Gabar Yamma da kogin Jordan wanda Isra'ila ke ci gaba da yiwa zagon kasa.
Blinken yace wasu kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta gabatar da sojoji da 'yan sandan da za su yi aikin samar da zaman lafiya a Gaza, kuma wadannan sun hada da wasu Falasdinwan da za'a tantance domin sanya su cikin aikin tsaron yankin.
Sakataren ya bayyana fatar ganin hukumomin Falasdinu sun nemi taimakon kasashen duniya wajen kafa hukumar mulki na riko wadda zata kula da bangarorin ci gaba na Falasdinawa da suka hada da bankuna da samar da ruwan sha da makamashi da kuma kula da lafiya.
Blinken yace Falasdinawan za su yi wannan aikin ne tare da Isra'ila da kuma tallafin kudade daga kasashen duniya, yayin da ake saran wani jami'in majalisar dinkin duniya ya shugabanci shirin bayan amincewar kwamitin sulhu.
Sakataren ya kara da cewar shugabannin da za su jagoranci yankin Gaza na riko za su fito ne daga cikin Falasdinawan dake Gaza da kuma wasu da kungiyar Falasdinu za ta gabatar tare da amincewar mutanen yankin, kuma za'a dora musu nauyin yiwa hukumar garambawul baki daya.
Yanzu haka ana ci gaba da tattaunawar kulla yarjejeniyar tsagaita wuta wanda ke samun goyan bayan shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden da kuma Donald Trump da ake saran ya karbi iko a kwanaki masu zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI