Isra'ila ta yi musayar fursunoni da kasar Siriya

Isra'ila ta yi musayar fursunoni da kasar Siriya

An sanar da cewa da shiga tsakanin kasar Rasha gwamnatin Bashar Asad da lsra'ila sun yi musayar fursunoni a tsakaninsu.

Kanfanin dillancin labaran SANA ce ta sanar da cewa tare da shiga tsakanin kasar Rasha gwamnatin Bashar Asad a Siriya na musayar fursunoni da kasar lsraila. 

A bisa wacannan yarjejeniyar za a kubutar da Siriyawa Nihal El Makt da Ziyad Kahmuz daga hannun lsraila. 

Haka kuma Siriya za ta saki wata yar lsraila da take tsare da ita.

Kamar yadda kafafen yada labaran kasar lsraila suka rawaito gwamnatin kasar ta nemi taimakon Rasha akan ayyanar da musayar fursunonin tsakaninta da Siriya.

 

 


News Source:   ()