Isra'ila ta bayar da umarnin kar a yi allurar riga-kafin Corona ga Falasdinawan da ta tsare

Isra'ila ta bayar da umarnin kar a yi allurar riga-kafin Corona ga Falasdinawan da ta tsare

Ministan Tsaron Al'uma na Isra'ila Amir Ohana ya bayar da umarnin kar a yi allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) ga Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen kurkukun Isra'ila.

Jaridar Haaretz ta bayar da labarin cewar, duk da ka'idojin Ma'aikatar Lafiya, amma Ministan Tsaron Al'uma Amir Ohana ya bayar da umarni ga hukumomin da lamarin ya shafa da kar a yi wa Falasdinawa da ke daure a gidajen kurkuku allurar riga-kafin Corona.

A umarnin da ya aike babu sunan "Falasdinawa", amma kuma a Isra'ila babu wasu da ake tsare da su saboda tsaro sai Falasdinawan.

Ana daur da mafi yaan Falasdinawa da ke gidajen kurkukun Isra'ila saboda matsala ta tsaro.

 


News Source:   ()