Sojojin Isra'ila sun sake kashe wata mace a yankin Zirin Gaza da ta yi wa kawanya tare da kai hare-haren ta'addanci.
Ya zuwa yanzu yanzu Falasdinawa 228 ne suka yi Shahada sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Zirin Gaza.
Jiragen saman Isra'ila na yaki sun yi ruwan bama-bamai a garuruwan Han Yunus da Refah dake Zirin Gaza.
A harin da aka kai a yankin Al-Satri na kudancin Han Yunus an kashe wata mace guda tare da jikkata wasu Falasdinawan 6.
A hare-haren da Isra'ila ta kai yankin fito na Han Yunus an jikkata wasu mutane, haka kuma a unguwar Japan dake garin an kai hari inda aka nufi wani gida a yankin Al-Shabura na Refah, amma ba a jikkata kowa ba.
Tun daga ranar 10 ga Mayu zuwa yau da azzalumar kasar Isra'ila ta fara kai hare-haren ta'addanci Zirin Gaza, Falasdinawa 228 da suka hada da yara kanana 64 da mata 37 sun yi Shahada, wasu dubu 1,620 kuma sun samu raunuka.